25. Ƙaƙa aka manta da sanannen birni,Birnin da take cike da murna?
26. A waccan rana samarinta za su fāɗi adandalinta.Za a hallaka sojojinta duka,Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
27. Zan kuma sa wuta a garun Dimashƙu,Za ta kuwa cinye fādodinBen-hadad.”
28. Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Kedar da sarakunan Hazor, waɗanda sarki Nebukadnezzar ya ci da yaƙi,“Ku tashi zuwa Kedar,Ku hallaka mutanen gabas.
29. Za a kwashe alfarwansu dagarkunansu,Da labulan alfarwansu, da dukankayansu.Za a kuma tafi da raƙumansu,Za a gaya musu cewa, ‘Razana takewaye ku!’
30. “Ku mazaunan Hazor, ku gudu zuwanesa,Ku ɓuya cikin zurfafa, ni Ubangiji nafaɗa,Gama Nebukadnezzar, SarkinBabila, ya shirya mukumaƙarƙashiya,Ya ƙulla mugun nufi game da ku.