38. Waɗannan shekaru ashirin da na yi tare da kai, tumakinka da awakinka ba su yi ɓari ba, ban kuwa ci ragunan garkenka ba.
39. Wanda namomin jeji suka yayyaga ban kawo maka ba, ni da kaina na ɗauki hasararsu. Ka kuma nemi abin da aka sace da rana ko da dare daga hannuna.
40. Abin da na zama ke nan, da rana na sha zafin rana, da dare kuwa na sha sanyi, ga rashin barci.
41. A waɗannan shekaru ashirin da nake cikin gidanka, na yi maka barantaka shekara goma sha huɗu domin 'ya'yanka mata biyu, shekara shida kuma domin garkenka, ka kuwa sauya ladana har sau goma.