46. “Idan jama'arka sun yi maka zunubi, gama ba mutumin da ba ya yin zunubi, har ka yi fushi da su, ka kuwa bashe su a hannun abokan gāba, har suka kwashe su zuwa bauta a wata ƙasa mai nisa,
47. idan sun koma cikin hankalinsu a ƙasar da aka kai su bauta, har suka tuba, suka roƙe ka a ƙasar, suna hurta zunubansu da irin muguntar da suka aikata, ka ji addu'arsu, ya Ubangiji.
48. Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu'a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka,
49. sai ka ji addu'arsu da roƙe-roƙensu daga Sama, wurin zamanka, ka amsa, ka ji ƙansu.
50. Ka gafarta dukan zunubansu, da tayarwar da suka yi maka. Ka sa abokan gabansu su ji tausayinsu.
51. Gama su jama'arka ne, mallakarka, waɗanda ka fito da su daga Masar, daga tsakiyar azaba.
52. “Ya Ubangiji Allah, ka dubi jama'arka Isra'ila da sarkinsu da idon rahama, ka kasa kunne gare su duk lokacin da suka yi roƙo a gare ka.
53. Gama ka keɓe su daga sauran dukan al'ummai domin su zama jama'arka kamar yadda ka faɗa ta bakin bawanka Musa, sa'ad da ka fito da kakanninmu daga Masar.”
54. Da Sulemanu ya gama wannan addu'a da roƙo ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda yake a durƙushe da hannuwansa a miƙe zuwa sama.
55. Ya tsaya, ya sa wa taron jama'ar Isra'ila albarka da babbar murya, ya ce,
56. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya hutar da jama'arsa, Isra'ilawa, bisa ga yadda ya alkawarta. Daga cikin abin da ya alkawarta duka na alheri ba ko ɗaya da bai cika ba, kamar yadda ya alkawarta wa bawansa, Musa.
57. Ya Ubangiji Allah, sai ka kasance tare da mu kamar yadda ka kasance tare da kakanninmu, kada ka rabu da mu, ko ka yashe mu.
58. Ka sa zukatanmu su juyo gare ka, mu yi tafiya cikin tafarkunka, mu kiyaye umarnanka, da ka'idodinka da dokokinka, waɗanda ka umarci kakanninmu.
59. Ya Ubangiji Allahnmu, ka sa wannan roƙo da na yi ya kasance a gabanka, dare da rana. Ka biya bukatar bawanka, da bukatar jama'arka, Isra'ila, ta kowace rana,
60. domin dukan al'umman duniya su sani Ubangiji shi kaɗai ne Allah, banda shi, ba wani.