21. A cikin Haikalin kuma na shirya wa akwatin alkawari wuri, inda alkawarin Ubangiji yake, wato alkawarin da ya yi wa kakanninmu sa'ad da ya fito da su daga ƙasar Masar.”
22. Sa'an nan Sulemanu ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron jama'ar Isra'ila. Ya ɗaga hannuwansa sama,
23. ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ba wani Allah kamarka cikin Sama a bisa, da cikin duniya a ƙasa, wanda yake cika alkawari, ya nuna ƙauna ga bayinsa, waɗanda suke tafiya a gabansa da zuciya ɗaya.
24. Kai wanda ka cika abin da ka faɗa wa bawanka, Dawuda, tsohona, i, abin da ka faɗa da bakinka ka cika shi yau.
25. Yanzu fa, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka cika wa bawanka Dawuda, tsohona, sauran abin da ka alkawarta masa, da ka ce, ‘Ba za ka rasa mutum a gabana wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai zuriyarka sun mai da hankali, sun yi tafiya a gabana kamar yadda kai ka yi.’
26. Yanzu fa, ya Allah na Isra'ila, sai ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka, Dawuda, tsohona.
27. “Amma ko Allah zai zauna a duniya? Ga shi, Saman sammai ba ta isa ta karɓe ka ba, balle wannan Haikali da na gina!
28. Duk da haka, ya Ubangiji Allahna, ka ji addu'ata, ni bawanka, da roƙe-roƙena, ka ji kukana da addu'ata da nake yi a gabanka yau.
29. Domin ka riƙa duban Haikalin nan dare da rana, wurin da ka ce sunanka zai kasance domin ka riƙa jin addu'ar da bawanka zai yi yana fuskantar wurin.
30. Sai ka riƙa jin roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra'ilawa, idan sun yi addu'a, suna fuskantar wurin nan, sa'ad da ka ji kuma, sai ka gafarta musu.
31. “Idan mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi, aka ba shi rantsuwa, idan ya zo, ya rantse a gaban bagadenka a wannan Haikali,
32. ya Ubangiji ka ji daga Sama, ka shara'anta bayinka, ka hukunta mai laifin, ka ɗora masa hakkinsa a kansa, amma ka kuɓutar da mara laifin, ka sāka masa bisa ga adalcinsa.
33. “Lokacin da abokan gāba suka ci mutanenka Isra'ila da yaƙi, saboda sun yi maka zunubi, idan sun komo wurinka, suka yabe ka, suka yi addu'a, suka roƙe ka a wannan Haikali,
34. sai ka ji daga Sama, ka gafarta wa jama'ar Isra'ila zunubinsu, sa'an nan ka sāke komar da su zuwa ƙasar da ka ba kakanninsu.
35. “Idan an hore su da rashin ruwan sama, saboda sun yi maka zunubi, idan sun tuba, suna fuskantar wannan Haikali, suka yi addu'a, suka kuma yabe ka,
36. sai ka ji daga Sama, ka gafarta zunuban sarki, da na jama'arka Isra'ila. Ka koya musu kyakkyawar hanyar da za su bi, ka sa a yi ruwan sama a ƙasarka wadda ka ba jama'arka gādo.
37. “Idan akwai yunwa a ƙasar, ko kuma akwai annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, sun cinye amfanin gona, idan kuma abokan gāba sun kawo wa jama'arka yaƙi har ƙofar birninsu, duk dai irin annoba da ciwon da yake cikinsu,
38. sai ka kasa kunne ga addu'arsu. Idan ɗaya daga cikin jama'arka Isra'ila ya matsu a zuciyarsa, ya ɗaga hannuwansa sama yana addu'a wajen wannan Haikali,
39. sai ka ji addu'arsa. Ka kasa kunne gare shi, a wurin zamanka a Sama, ka gafarta masa. Kai kaɗai ka san tunanin dukan mutane. Ka yi da kowa bisa ga abin da ya yi,
40. domin mutanenka su yi tsoronka a dukan kwanakinsu a ƙasar da ka ba kakanninmu.
41. “Sa'ad da kuma baƙo wanda yake wata ƙasa mai nisa ya ji labarin sunanka,