1 Sar 17:22-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Ubangiji kuwa ya amsa wa Iliya, ran yaron ya komo cikinsa, sai ya farfaɗo.

23. Iliya ya ɗauki yaron ya sauko da shi daga soro, ya kai shi cikin gida, ya ba uwar. Ya ce mata, “Ki gani, ɗanki yana da rai.”

24. Sai macen ta ce wa Iliya, “Yanzu na sani kai mutumin Allah ne, Ubangiji kuwa yana magana ta wurinka.”

1 Sar 17