Zak 10:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku roƙi ruwan sama daga wurin Ubangiji a lokacin bazara,Gama Ubangiji ne yake yin gizagizan hadiri,Shi ne yake bai wa mutane yayyafi.Shi ne kuma yake ba kowane mutum tsire-tsiren saura.

2. Gama maganar shirme kan gida yake yi,Masu dūba suna ganin wahayin ƙarya,Masu mafarkai suna faɗar ƙarya,Ta'aziyyarsu ta banza ce.Domin haka mutane suna ta yawo kamar tumaki,Suna shan wahala saboda rashin makiyayi.

3. Ubangiji ya ce,“Ina fushi ƙwarai da makiyayan,Zan kuwa hukunta shugabannin,Gama ni Ubangiji Mai Runduna zan lura da garkena,Wato jama'ar Yahuza.Zan mai da su dawakaina na yaƙi.

Zak 10