Zab 132:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, kada ka manta da DawudaDa dukan irin aikin da ya yi.

2. Ka tuna, ya Ubangiji, da alkawarin da ya yi,Da rantsuwar da ya yi maka, ya Maɗaukaki, Allah na Isra'ila,

3. “Ba zan tafi gida ko in kwanta ba,

4. Ba zan huta, ko in yi barci ba,

5. Sai sa'ad da na shirya wa Ubangiji wuri,Wato Haikali domin Maɗaukaki, Allah na Isra'ila.”

6. Mun ji labari akwatin alkawari yana Baitalami,Amma muka same shi a kurmi.

7. Muka ce, “Bari mu tafi Haikalin Ubangiji,Mu yi sujada a gaban kursiyinsa!”

Zab 132