Mat 22:27-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Bayansu duka sai matar ta rasu.

28. To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu, su bakwai ɗin? Don duk sun aure ta.”

29. Amma Yesu ya amsa musu ya ce, “Kun ɓăta ne, domin ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba.

30. Domin a tashin matattu, ba a aure, ba a aurarwa, sai dai kamar mala'ikun da suke Sama ake.

31. Game da tashin matattu, ashe, ba ku taɓa karanta abin da Allah ya ce muku ba? cewa,

32. ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.’ Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.”

33. Da jama'a suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.

34. Amma da Farisiyawa suka ji ya ƙure Sadukiyawa, suka taru.

35. Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Attaura, ya yi masa tambaya, yana gwada shi, ya ce,

36. “Malam, wane umarni ne mafi girma a cikin Attaura?”

37. Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.

38. Wannan shi ne babban umarni na farko.

39. Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’

40. A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.”

41. Tun Farisiyawa suna tare gu ɗaya, sai Yesu ya yi musu tambaya,

42. ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.”

Mat 22