16. In kuwa bai saurare ka ba, sai ka tafi da mutum ɗaya ko biyu, don a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.
17. In kuma ya ƙi sauraronsu, sai ka shaida wa ikilisiya. In kuma har ya ƙi sauraron ikilisiyar, ka maishe shi kamar bare, ko mai karɓar haraji.”
18. “Hakika, ina gaya muku, kome kuka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome kuka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne.
19. Har wa yau dai ina gaya muku, in mutum biyu daga cikinku, ra'ayinsu ya zo ɗaya a nan duniya a kan wani abin da za su roƙa, Ubana kuwa da yake Sama zai yi musu shi.
20. Gama kuwa inda mutum biyu ko uku suka taru saboda sunana, ni ma ina nan a tsakiyarsu.”
21. Sai Bitrus ya matso ya ce masa, “Ya Ubangiji, sau nawa ɗan'uwana zai yi mini laifi in yafe masa? Har sau bakwai?”
22. Yesu ya ce masa, “Ba sau bakwai kawai na ce maka ba, sai dai bakwai har saba'in.
23. “Saboda haka za a misalta Mulkin Sama da wani sarkin da yake so ya yi ƙididdigar dukiyarsa da yake hannun bayinsa.
24. Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wanda yake bi talanti dubu goma bashi.
25. Da yake ya gagara biya, sai ubangidansa ya yi umarni a sayar da shi da mata tasa da 'ya'yansa da kuma duk abin da ya mallaka, a biya kuɗin.
26. Sai bawan ya faɗi a gabansa ya yi masa ladabi, ya ce, ‘Ya ubangida, ka yi mini haƙuri, zan biya ka tsaf.’
27. Saboda tausayin bawan nan ubangidansa ya sake shi, ya yafe masa bashin.
28. Amma wannan bawa, da fitarsa sai ya tarar da wani abokin bautarsa, wanda yake bi dinari ɗari bashi. Ya cafi wuyarsa, ya ce, ‘Biya ni abin da nake binka.’
29. Sai abokin bautarsa ya faɗi a gabansa, ya yi ta roƙonsa ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, ai, zan biya ka.’