12. Iyakar kuma za ta gangara har zuwa Urdun, ta tsaya a Tekun Gishiri. Wannan ita ce ƙasarsu da iyakokinta kewaye da ita.
13. Sai Musa ya ce wa Isra'ilawa, “Wannan ita ce ƙasar da za ku gāda ta hanyar jefa kuri'a. Ƙasar da Ubangiji ya umarta a ba kabilai tara da rabi.
14. Gama kabilar Ra'ubainu da ta Gad da kuma rabin kabilar Manassa sun riga sun karɓi nasu gādo.
15. Kabilan nan biyu da rabi sun karɓi nasu gādo a wancan hayin Urdun a gabashin Yariko.”