23. Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji yana tsaye kan hanya da takobi zare a hannunsa, sai ta kauce daga hanya, ta shiga saura. Bal'amu kuwa ya buge ta don ya komar da ita a hanyar.
24. Sai mala'ikan Ubangiji ya je, ya tsaya a inda hanyar ta yi matsatsi a tsakanin bangayen gonakin inabi.
25. Sa'ad da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji, ta matsa a jikin bango, ta goge ƙafar Bal'amu ga bangon, sai ya sāke bugunta.
26. Mala'ikan Ubangiji kuma ya sha kanta, ya tsaya a ƙunƙuntaccen wuri inda ba wurin juyawa zuwa dama ko hagu.
27. Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji, sai ta kwanta a ƙafafun Bal'amu. Sai Bal'amu ya husata, ya bugi jakar da sandansa.
28. Ubangiji kuwa ya buɗe bakin jakar, ta ce wa Bal'amu, “Me na yi maka, da ka buge ni har sau uku?”
29. Bal'amu ya ce mata, “Domin kin shashantar da ni, da a ce ina da takobi a hannuna, da na kashe ki.”
30. Sai jakar ta ce wa Bal'amu, “Ba ni ce jakarka ba wadda kake ta hawa dukan lokacin nan har zuwa yau? Na taɓa yi maka haka?”Ya ce, “A'a.”