20. Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga 'yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”
21. Mutane za su yi ta kai da kawowa a ko'ina cikin ƙasar, cikin matsuwa da yunwa. A yunwar da suke sha da haushin da suke ji, za su zagi sarkinsu, su kuma zagi Allahnsu. Har ma zai yiwu su ɗaga ido su dubi sararin sama,
22. ko su zura wa ƙasa ido, amma ba abin da za su gani, sai wahala da duhu mai banrazana, inda za a kora su a ciki.