6. Sojojin ƙasar Elam sun zo kan dawakai suna rataye da kwari da baka. Sojojin ƙasar Kir sun shirya garkuwoyinsu.
7. Kwarurukansu masu dausayi na ƙasar Yahuza suna cike da karusai, sojoji kuma a kan dawakai suna tsattsaye a ƙofofin Urushalima.
8. Dukan kagaran Yahuza sun rushe.Sa'ad da wannan ya faru kun kwaso makamai daga cikin taskar makamai.
11. kun gina matarar ruwa a jikin garuka don ta tare ruwan da yake gangarowa daga tsohon tafki. Amma ba ku kula da Allah ba, wanda ya shirya wannan tuntuni, wanda kuma ya sa wannan ya kasance.
12. Ubangiji Mai Runduna yana kiranku ku yi kuka, ku yi makoki, ku aske kawunanku, ku sa tsummoki.
13. A maimakon haka sai kuka yi dariya, kuka yi biki. Kuka yanka tumaki da shanu don ku ci, kuka sha ruwan inabi. Kuka ce, “Gara mu ci mu sha! Gobe za mu mutu.”
14. Ubangiji Mai Runduna ya ce mini, “Ko kusa ba za a gafarta musu wannan mugunta ba muddin ransu. Ni, Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”