Irm 48:18-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ku da kuke zaune a Dibon,Ku sauka daga wurin zamanku maidaraja,Ku zauna a busasshiyar ƙasa,Gama mai hallaka Mowab ya zo yayi gab da ku.Ya riga ya rushe kagararku.

19. Ku mazaunan Arower,Ku tsaya a kan hanya, ku jira,Ku tambayi wanda yake guduDa wanda yake tserewa,Abin da ya faru.

20. An kunyatar da Mowab, ta rushe.Ku yi kuka dominta,Ku faɗa a Arnon, cewa Mowab tahalaka.

21. “Hukunci ya auka kan garuruwan da suke a ƙasar fili, wato Holon, da Yahaza, da Mefayat,

22. da Dibon, da Nebo, da Bet-diblatayim,

23. da Kiriyatayim, da Bet-gamal, da Ba'almeyon,

Irm 48