Irm 16:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. “Sa'ad da ka faɗa wa mutanen nan wannan magana duka, za su kuwa ce maka, ‘Me ya sa Ubangiji ya hurta wannan babbar masifa a kanmu? Mene ne laifinmu? Wane irin zunubi muka yi wa Ubangiji Allahnmu?’

11. Sai ka faɗa musu cewa, Ubangiji ya ce, ‘Domin kakanninku sun rabu da ni, sun bi gumaka, sun bauta musu, sun yi musu sujada. Sun rabu da ni, sun ƙi kiyaye dokokina.

12. Ku kuma kun yi laifi fiye da na kakanninku. Kowannenku kuwa ya bi tattauran mugun nufin zuciyarsa, yana ƙin kasa kunne gare ni.

13. Don haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasa wadda ku ko kakanninku ba ku sani ba. A can za ku bauta wa gumaka dare da rana, gama ba zan nuna muku ƙauna ba.’

Irm 16