Irm 15:15-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sa'an nan Irmiya ya ce, “YaUbangiji, ka sani.Kai ne, ka ziyarce ni,Ka kuma sāka wa waɗanda suketsananta mini.Ka sani saboda kai nake shan zargi.

16. Maganarka da na samu na ci.Maganarka kuwa ta zama abarmurna a gare ni,Ta faranta mini zuciya.Gama ana kirana da sunanka,Ya Ubangiji Allah Mai Runduna.

17. Ban zauna cikin ƙungiyar masuannashuwa ba.Ban kuwa yi murna ba,Na zauna ni kaɗai saboda kana tareda ni,Gama ka sa na cika da haushi.

18. Me ya sa azabata ta ƙi ƙarewa,Raunukana kuma ba su warkuwa,Sun kuwa ƙi warkewa?Za ka yaudare ni kamar rafi,Ko kamar ruwa mai ƙafewa?”

Irm 15