7. Lokacin da na fito da kakanninsu daga ƙasar Masar na faɗakar da su musamman, na yi ta faɗakar da su har wannan rana, ina cewa, ‘Ku yi biyayya da maganata.’
8. Amma duk da haka ba su yi biyayya ba, ba su kuma kasa kunne ba. Kowa ya bi tattaurar zuciyarsa mai mugunta. Domin haka na kawo musu dukan maganar alkawarin nan wanda na umarce su su yi, amma ba su yi ba.”
9. Ubangiji ya kuma ce mini, “Akwai tawaye a cikin mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima.
10. Sun koma a kan laifofin kakanninsu, waɗanda suka ƙi jin maganata, suka bi gumakansu don su bauta musu, jama'ar Isra'ila da na Yahuza sun ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu.
11. Saboda haka ni Ubangiji na ce, ‘Ga shi, ina kawo musu masifa wadda ba za su iya tsere mata ba, ko da za su yi kuka gare ni ba zan ji su ba.
12. Sa'an nan biranen Yahuza da mazaunan Urushalima za su tafi, su yi kuka ga gumaka waɗanda suka ƙona musu turare, amma ba za su iya cetonsu a lokacin wahalarsu ba.