Irm 11:22-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Domin haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ga shi kuwa, zan hukunta su, za a kashe samarinsu da takobi, 'ya'yansu mata da maza, yunwa za ta kashe su.

23. Ba wanda zai ragu daga cikin mutanen Anatot, gama zan kawo wa mutanen Anatot masifa, a shekarar hukuncinsu.”

Irm 11