21. Makiyayan dakikai ne,Ba su roƙi Ubangiji ba,Don haka ba su sami wadata ba,An watsa dukan garkensu.
22. Ku ji fa, an ji ƙishin-ƙishin! Ga shikuma, yana tafe.Akwai babban hargitsin da ya fitodaga arewa,Don a mai da biranen Yahuza kufai,wurin zaman diloli.
23. “Ya Ubangiji, na sani al'amuranmutum ba a hannunsa suke ba,Ba mutum ne yake kiyaye takawarsaba
24. Ka tsauta mini, ya Ubangiji, ammada adalcinka,Ba da fushinka ba, don kada kawofinta ni.
25. Ka kwarara hasalarka a kan sauranal'umma da ba su san ka ba,Da a kan jama'ar da ba su kiransunanka,Gama sun cinye Yakubu,Sun cinye shi, sun haɗiye shi,Sun kuma mai da wurin zamansakufai.”