17. Mutumin ya ce, “Sun riga sun tashi daga nan, gama na ji sun ce, ‘Bari mu tafi Dotan.’ ” Saboda haka, Yusufu ya bi sawun 'yan'uwansa, ya kuwa same su a Dotan.
18. Da suka hango shi daga nesa, kafin ya zo kusa da su, sai suka ƙulla su kashe shi.
19. Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can yana zuwa.
20. Ku zo mu kashe shi yanzu, mu jefa shi cikin ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, sa'an nan mu ce, wata muguwar dabbar jeji ce ta kashe shi, sa'an nan mu ga yadda mafarkinsa zai zama.”
21. Amma sa'ad da Ra'ubainu ya ji, ya yi ƙoƙari ya cece shi daga hannunsu, yana cewa, “Kada mu raba shi da ransa.
22. Kada mu kashe shi, mu dai jefa shi cikin rijiyan nan a jeji, amma kada mu yi masa lahani.” Ya yi haka da nufin ya cece shi daga hannunsu, ya mayar da shi ga mahaifinsu.
23. Don haka, sa'ad da Yusufu ya zo wurin 'yan'uwansa, suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai ado wadda take wuyansa.