Far 37:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yakubu ya zauna a ƙasar Kan'ana inda mahaifinsa ya yi baƙunci.

2. Wannan shi ne tarihin zuriyar Yakubu.Yusufu yana da shekara goma sha bakwai sa'ad da ya zama makiyayin garke tare da 'yan'uwansa, ɗan ƙanƙanen yaro ne a tsakanin 'ya'ya maza na Bilha da Zilfa matan mahaifinsa. Sai Yusufu ya kawo labarin munanan abubuwa da 'yan'uwansa suke yi a wurin mahaifinsa,

3. Isra'ila kuwa ya fi ƙaunar Yusufu da kowannensu, domin shi ɗan tsufansa ne. Sai ya yi masa riga mai ado.

4. Amma sa'ad da 'yan'uwansa suka gane mahaifinsu yana ƙaunarsa fiye da dukansu, suka ƙi jininsa, ba su iya maganar alheri da shi.

5. Yusufu ya yi mafarki. Sa'ad da ya faɗa wa 'yan'uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.

Far 37