Ez 5:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ga shi, ta tayar wa ka'idodina da muguwar tayarwa fiye da al'ummai, ta kuma tayar wa dokokina fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da ita. Ta ƙi bin ka'idodina, ta kuma ƙi ta yi tafiya bisa ga dokokina.

7. Domin haka ni na ce, ‘Da yake kin cika rikici fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da suke, kin ƙi yin tafiya cikin dokokina, ba ki kiyaye ka'idodin ba, amma kin bi ka'ikodin al'umman da take kewaye da ke,

8. to, ina gāba da ke, zan hukunta ki a idanun al'ummai.

9. Saboda yawan abubuwa masu banƙyama da kika aikata, zan yi miki abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan sāke yin irinsa ba.

10. Ubanni za su cinye 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko'ina.

Ez 5