Ez 37:13-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Mutanena za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na buɗe kaburburansu na tashe su daga cikinsu.

14. Zan sa Ruhuna a cikinsu za su kuwa rayu. Zan sa su a ƙasarsu sa'an nan za su sani ni Ubangiji na faɗa, na kuwa aikata.”

15. Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,

16. “Ɗan mutum, ka ɗauki sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yahuza da magoyan bayansa.’ Ka kuma ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yusufu, sandan Ifraimu, da dukan mutanen Isra'ila, magoyan bayansa.’

17. Ka haɗa su su zama sanda guda a hannunka.

18. Sa'ad da kuma jama'arka suka ce maka ka nuna musu abin da kake nufi da waɗannan,

19. sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce zan karɓe sandan Yusufu, wanda yake a hannun Ifraimu da mutanen Isra'ila magoyan bayansa, in haɗa shi da sandan Yahuza in maishe su sanda guda a hannuna.

20. “Sa'ad da sandunan da ka yi rubutu a kansu suna hannunka a gabansu,

21. sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce, zan komo da jama'ar Isra'ila daga wurin al'ummai inda suka warwatsu, zan tattaro su daga ko'ina, in maido su ƙasarsu.

22. Zan maishe su al'umma guda a ƙasar Isra'ila. Sarki ɗaya zai sarauce su duka, ba za su ƙara zama al'umma biyu ba, ba kuwa za su ƙara zama masarauta biyu ba.

23. Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da abubuwan banƙyama da kowane irin laifi ba. Zan komo da su daga riddar da suka yi, in tsarkake su. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu.

Ez 37