27. Sai ya tashi ya tafi. Ga wani mutumin Habasha, wani bābā, mai babban matsayi a mulkin Kandakatu, sarauniyar Habasha, shi ne kuwa ma'ajinta, ya zo Urushalima ne yin sujada,
28. yana komawa gida a zaune a cikin keken dokinsa, yana karatun littafin Annabi Ishaya.
29. Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa ka yi kusa da keken dokin nan.”
30. Sai Filibus ya yi gudu zuwa wurinsa, ya ji shi yana karatun littafin Annabi Ishaya. Ya ce, “Kana kuwa fahimtar abin da kake karantawa?”
31. Sai ya ce, “Ina fa? Sai ko wani ya fassara mini.” Sai ya roƙi Filibus ya hau su zauna tare.