17. Ya kuma rubuta wasiƙu, ya zargi Ubangiji Allah na Isra'ila, ya yi maganar saɓo, yana cewa, “Kamar yadda gumakan al'umman sauran ƙasashe suka kāsa ceton jama'arsu daga hannuna, haka nan kuma Allahn Hezekiya ba zai iya ceton jama'arsa daga hannuna ba.”
18. Da babbar murya, da Yahudanci kuwa, suka yi ta yin magana da jama'ar Urushalima waɗanda suke kan garu, don a tsoratar da su, a kuma firgita su, don su ci birnin.
19. Suka yi ta magana a kan Allah na Urushalima, kamar yadda suka yi magana a kan gumakan al'ummai, wato aikin hannuwan mutane.
20. Sai sarki Hezekiya, da annabi Ishaya ɗan Amoz, suka yi addu'a saboda wannan al'amari, suka yi kuka zuwa Sama.
21. Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.
22. Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mazaunan Urushalima daga hannun Sennakerib Sarkin Assuriya, daga kuma hannun dukan maƙiyansa, ya hutar da su ta kowace fuska.
23. Mutane da yawa suka kawo wa Ubangiji sadakoki a Urushalima, suna kuma kawo wa Hezekiya Sarkin Yahuza abubuwa masu daraja. Saboda haka ya sami ɗaukaka a idon dukan sauran al'ummai, tun daga wannan lokaci har zuwa gaba.
24. A kwanakin nan kuwa Hezekiya ya yi ciwo gab da mutuwa, sai ya yi addu'a ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya amsa masa ya ba shi alama.
25. Amma Hezekiya bai nuna godiya a kan amfanin da ya samu ba, saboda girmankai. Saboda haka hasala ta auka kansa, da kan Yahuza da Urushalima.