2 Tar 30:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Gama idan kun juyo zuwa ga Ubangiji, 'yan'uwanku da 'ya'yanku za su sami rahamar waɗanda suka kama su, su komo wannan ƙasa. Gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne, mai jinƙai, ba zai kawar da fuskarsa daga gare ku ba, idan kun komo gare shi.”

10. Manzannin fa suka tafi gari gari a ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, har zuwa Zabaluna, amma suka yi musu dariyar raini, suka yi musu ba'a.

11. Sai mutane kaɗan na Ashiru, da na Manassa, da na Zabaluna suka yi tawali'u, suka zo Urushalima.

12. Ikon Allah kuma yana kan Yahuza, ya ba su zuciya ɗaya ta su yi abin da sarki da sarakunansa suka umarta bisa ga maganar Ubangiji.

13. Mutane da yawa kuwa suka zo Urushalima don su yi idin abinci marar yisti a wata na biyu, aka yi babban taro.

14. Sai suka kama aiki, suka kawar da bagadan da suke cikin Urushalima, da dukan bagadan ƙona turare suka kwashe suka zubar a kwarin Kidron.

15. Suka yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Suka sa firistoci da Lawiyawa su sha kunya, saboda haka sai suka tsarkake kansu, suka kawo hadayu na ƙonawa a Haikalin Ubangiji.

16. Sai suka ɗauki matsayinsu wanda aka ayyana bisa ga dokar Musa, mutumin Allah, firistocin suka yarfa jinin da suka karɓa daga hannun Lawiyawa.

2 Tar 30