1. Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha 'yar Zadok.
2. Ya aikata abin da yake daidai saboda Ubangiji, kamar dukan abin da tsohonsa Azariya ya yi, sai dai bai kutsa cikin Haikalin Ubangiji ba. Amma jama'a suka ci gaba da aikata rashin kirki.
3. Ya gina ƙofar bisa, ta Haikalin Ubangiji, ya yi gine-gine masu yawa a garun Ofel.
4. Ya kuma gina birane a ƙasar tuddai ta Yahuza, da kagara, da hasumiya a tuddai masu kuramu.