2 Tar 24:25-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Sa'ad da suka tafi, sun bar shi da rauni mai tsanani ƙwarai, sai barorinsa suka yi masa maƙarƙashiya suka kashe shi a gadonsa, saboda ya kashe ɗan Yehoyada firist. Ya mutu, aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba su binne shi a kabarin sarakuna ba.

26. Waɗannan su ne waɗanda suka yi masa maƙarƙashiyar, Yozakar ɗan Shimeyat wata Ba'ammoniya, da Yehozabad ɗan Shimrit wata mutuniyar Mowab.

27. Labarin 'ya'yansa maza da annabcin da aka kawo a kansa da labarin sāke ginin Haikalin Allah, an rubuta su a sharhin littafin sarakunan. Sai Amaziya ɗan Yowash ya gāji gadon sarautarsa.

2 Tar 24