2 Tar 21:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yehoshafat ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda tare da kakanninsa, ɗansa kuma ya gāji gadon sarautarsa.

2. Yoram yana da 'yan'uwa maza, su ne Azariya, da Yehiyel, da Zakariya, da Azariya, da Maikel da kuma Shefatiya. Waɗannan 'ya'ya maza ne na Yehoshafat, Sarkin Yahuza.

3. Tsohonsu ya ba su kyautai da yawa na azurfa da zinariya, da abubuwa masu daraja, da birane masu garu a Yahuza, amma ya ba da mulkin ga Yoram, saboda shi ne ɗan fari.

4. Sa'ad da Yoram ya hau gadon sarautar tsohonsa, ya kahu sosai, sai ya karkashe dukan 'yan'uwansa da takobi, ya kuma karkashe waɗansu daga cikin sarakunan Yahuza.

5. Yoram yana da shekara talatin da biyu sa'ad da ya hau gadon sarauta, ya kuwa yi mulki a Urushalima shekara takwas.

6. Ya yi yadda sarakunan Isra'ila suka yi, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama matarsa 'yar Ahab ce. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji.

2 Tar 21