2 Sam 3:8-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Abner ya husata saboda wannan magana, ya ce, “Kana zato ni maci amanar ƙasa ne? Kana tsammani ina wa ƙasar Yahuza aiki ne? Tun da farko ina ta nuna alheri ga gidan Saul, tsohonka, da 'yan'uwansa, da abokansa, ban kuwa ba da ka a hannun Dawuda ba. Amma ga shi, yau ka zarge ni da laifin kwartanci game da wannan mata.

9. Allah ya la'anta ni, idan ban yi wa Dawuda abin da Ubangiji ya rantse masa ba,

10. wato in mayar wa Dawuda da sarautar gidan Saul. In kafa kursiyin Dawuda a kan Isra'ila da kan Yahuza tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba.”

11. Ish-boshet kuwa bai ce wa Abner uffan ba, don yana jin tsoronsa.

12. Sai Abner ya aiki manzanni zuwa wurin Dawuda a Hebron, ya ce, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi mini alkawari, ni kuwa zan goyi bayanka, in sa dukkan Isra'ilawa su bi ka.”

13. Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi maka alkawari a kan wannan sharaɗi, ba za ka ga fuskata ba sai ka kawo mini matata, Mikal, 'yar Saul, sa'ad da za ka zo wurina.”

2 Sam 3