1. Sa'ad da Dawuda ya wuce ƙwanƙolin dutsen kaɗan, sai ga Ziba baran Mefiboshet ya sadu da shi. Ya zo da jaki biyu ya yi musu labtu da gurasa dunƙule ɗari biyu, da zabibi ɗari, da sababbin 'ya'yan itace guda ɗari, da salkar ruwan inabi.
2. Sarki kuwa ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo abubuwan nan?”Ziba ya amsa, ya ce, “An kawo wa iyalin sarki jakuna su hau, da abinci, da 'ya'yan itace, domin samari su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suke rafkewa a jejin su sha.”