14. 'Ya'yan Manassa, maza, su ne Asriyel, wanda ƙwarƙwararsa Ba'aramiya ta haifa masa. Ta kuma haifi Makir mahaifin Gileyad.
15. Makir ya auro wa Huffim da Shuffim mata. Sunan 'yar'uwarsa Ma'aka, sunan ɗan'uwansa kuwa Zelofehad, Zelofehad yana da 'ya'ya mata kaɗai.
16. Sai Ma'aka matar Makir ta haifi ɗa, ta sa masa suna Feres, sunan ɗan'uwansa kuwa Sheres. 'Ya'yan Feres maza, su ne Ulam da Rakem.
17. Ɗan Ulam shi ne Bedan. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Gileyad ɗan Makir, jīkan Manassa.
18. 'Yar'uwarsa, Hammoleket ta haifi Ishodi, da Abiyezer, da Mala.
19. 'Ya'yan Shemida, maza, su ne Ahiyan, da Shekem, da Liki, da Aniyam.