1 Sar 14:27-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. A maimakonsu kuwa sarki Rehobowam ya yi garkuwoyin tagulla, ya sa a hannun shugabannin masu tsaro waɗanda suke tsaron ƙofar gidan sarki.

28. Duk lokacin da sarki ya shiga Haikalin Ubangiji, sai matsara su ɗauki garkuwoyin, su kuma mayar da su a ɗakin tsaro.

29. Sauran ayyukan Rehobowam, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

30. Kullum akan yi ta yin yaƙi tsakanin Rehobowam da Yerobowam,

31. Rehobowam kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce. Ɗansa, Abaija ya gāji sarautar.

1 Sar 14