1 Kor 15:35-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Watakila wani zai yi tambaya, “Ta yaya ake ta da matattu? Da wace irin kama kuma suke fitowa?”

36. Kai, marar azanci! Abin da ka shuka, ai, ba zai tsiro ba sai ya mutu.

37. Abin da ka shuka kuma, ba shi ne ainihin abin da zai kasance ba, ƙwaya ce ƙawai, ko ta alkama ce, ko kuma, wata iri dabam.

38. Amma Allah yakan ba ta kama, yadda ya nufa, kowace ƙwaya da irin tata kama.

39. Don ba dukan tsoka ce iri ɗaya ba, mutane da irin tasu, dabbobi ma da irin tasu, tsuntsaye da irin tasu, kifaye kuma da irin tasu.

40. Akwai halitta irin ta Sama, akwai kuma irin ta ƙasa. Amma ɗaukakar irin ta Sama dabam, ɗaukakar irin ta ƙasa kuma dabam.

41. Ɗaukakar rana dabam, ta wata dabam, ta taurari kuma dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen ɗaukaka.

1 Kor 15