1 Bit 3:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar 'yan'uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali'u.

9. Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.

10. Domin,“Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri,Sai ya kame bakinsa daga ɓarna,Ya kuma hana shi maganar yaudara.

11. Ya rabu da mugunta,ya kama nagarta,Ya himmantu ga zaman lafiya, ya kuma dimance ta.

12. Gama Ubangiji yana lura da masu aikata adalci,Yana kuma sauraron roƙonsu.Amma Ubangiji yana gāba da masu aikata mugunta.”

1 Bit 3