Zak 7:13-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Kamar yadda na yi kira suka ƙi ji, haka kuma suka yi kira, ni ma na ƙi ji.

14. Na sa guguwa ta warwatsa su a cikin al'ummai da ba su san su ba. Ƙasar da suka bari ta zama kango, ba mai kai da kawowa a cikinta. Ƙasa mai kyau ta zama kango.”

Zak 7