Zak 7:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A rana ta huɗu ga watan tara, wato watan Kisle, a shekara ta huɗu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da Zakariya.

2. Sai mutanen Betel suka aiki Sharezer da Regem-melek da mutanensu su nemi tagomashi a wurin Ubangiji,

3. su kuma tambayi firistocin Haikalin Ubangiji da annabawa, cewa ko ya kamata su yi baƙin ciki da azumi a watan biyar kamar yadda suka saba yi a shekarun baya?

4. Sa'an nan Ubangiji Mai Runduna ya yi mini magana, ya ce,

Zak 7