1. Ga ranar Ubangiji tana zuwa sa'ad da za a raba ganimar da aka ƙwace daga gare ku a kan idonku.
2. Gama zan tattara dukan al'ummai su yi yaƙi da Urushalima. Za a ci birnin, a washe gidajen. Za a yi wa mata faɗe. Za a kai rabin mutanen birnin bauta, amma za a bar sauran mutanen a cikin birnin.