Zak 12:12-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Kowane iyali a ƙasar za su yi makokinsu a keɓe, iyalin gidan Dawuda kuma za su yi nasu a keɓe, matansu za su yi nasu a keɓe. Iyalin gidan Natan su ma za su yi nasu makoki a keɓe, matansu kuma a keɓe.

13. Iyalin gidan Lawi za su yi makokinsu a keɓe, matansu kuma a keɓe. Iyalin gidan mutanen Shimai za su yi makokinsu a keɓe, matansu kuma a keɓe.

14. Sauran dukan iyalan da suka ragu za su yi nasu makoki a keɓe, matansu kuma a keɓe.”

Zak 12