Zab 97:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji Sarki ne! Ki yi murna ke duniya!Ku yi murna, dukanku tsibiran da suke cikin tekuna!

2. Gajimare da duhu sun kewaye shi.A kan adalci da gaskiya ya kafa mulkinsa.

3. Wuta tana tafe a gabansa, tana cinye maƙiyansaWaɗanda suke kewaye da shi.

4. Walƙiyarsa ta haskaka duniya,Duniya kuwa ta gani ta yi ta rawar jiki.

Zab 97