4. Ubangiji da girma yake, tilas a ɗaukaka shi,Tilas a fi jin tsoronsa fiye da dukan alloli.
5. Allolin dukan al'ummai, gumaka ne kawai,Amma Ubangiji ne ya yi sammai.
6. Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi,Girma da jamali suna cikin Haikalinsa.
7. Dukan jama'ar da suke bisa duniya su yabi Ubangiji!Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!
8. Ku yabi sunan Ubangiji mai ɗaukaka,Ku kawo sadaka, ku shiga Haikalinsa.