Zab 95:6-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ku zo, mu durƙusa, mu yi masa sujada,Mu durƙusa a gaban Ubangiji, Mahaliccinmu!

7. Shi ne Allahnmu,Mu ne jama'ar da yake lura da ita,Mu ne kuma garken da yake ciyarwa.Yau ku ji abin da yake faɗa.

8. “Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba,Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.

Zab 95