2. Kursiyinka, ya Ubangiji, ya kahu tun daga farko,Kana nan tun fil azal.
3. Ya Ubangiji, zurfafan teku suna ta da muryarsu,Suna ta da muryarsu da ruri.
4. Ubangiji yana mulki cikin Sama,Mulkinsa mafifici ne,Fiye da rurin teku,Fiye da ikon raƙuman ruwan teku.
5. Dokokinka dawwamammu ne, ya Ubangiji,Haikalinka kuwa tsattsarka ne ƙwarai,Har abada abadin.