Zab 91:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ko annobar da take aukowa da dare,Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana.

7. Mutum dubu za su fāɗi daura da kai,Dubu goma kuma za su fāɗi dama da kai,Amma kai, ba za a cuce ka ba.

8. Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye.

9. Domin ka ɗauka Ubangiji yake kiyaye ka,Maɗaukaki ne yake tsaronka,

10. To, ba bala'in da zai same ka,Ba za a yi wa gidanka aikin ƙarfi da yaji ba.

11. Allah zai sa mala'ikunsa su lura da kai,Za su kiyaye ka duk inda za ka tafi.

12. Za su ɗauke ka a hannuwansu,Don kada ka buga ƙafarka a dutse.

13. Za ka tattake zakoki da macizai,Za ka tattake zakoki masu zafin raiDa macizai masu dafi.

Zab 91