3. Hakika zai kiyaye kaDaga dukan hatsarorin da ka ɓoye,Daga kuma dukan mugayen cuce-cuce.
4. Zai rufe ka da fikafikansa,Za ka zauna lafiya a ƙarƙashinsu.Amincinsa zai tsare ka, ya kiyaye ka.
5. Ba za ka ji tsoron hatsarori da dare ba,Ko fāɗawar da za a yi maka da rana,
6. Ko annobar da take aukowa da dare,Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana.
7. Mutum dubu za su fāɗi daura da kai,Dubu goma kuma za su fāɗi dama da kai,Amma kai, ba za a cuce ka ba.
8. Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye.