Zab 89:38-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Amma kana fushi da zaɓaɓɓen sarkinka,Ka rabu da shi, ka yashe shi.

39. Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka,Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.

40. Ka rurrushe garun birninsa,Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.

41. Dukan waɗanda suke wucewa za su sace masa kayansa,Maƙwabtansa duka suna yi masa ba'a.

42. Ka ba maƙiyansa nasara,Ka sa dukansu su yi murna.

43. Ka sa makamansa su zama marasa amfani,Ka bari a ci shi da yaƙi.

44. Ka ƙwace masa sandan sarautarsa,Ka buge gadon sarautarsa ƙasa.

45. Ka sa shi ya tsofe kafin lokacinsa,Ka rufe shi da kunya.

46. Har yaushe za ka ɓoye kanka, ya Ubangiji?Har abada ne?Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta?

Zab 89