Zab 85:9-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Hakika a shirye yake yă ceci waɗanda suke girmama shi,Kasancewarsa a ƙasar, ceto ne ga ƙasar.

10. Ƙauna da aminci za su sadu wuri ɗaya,Adalci da salama za su gamu.

11. Amincin mutum zai yunƙura daga duniya, yă nufi sama.Adalcin Allah kuwa zai dubo daga Sama.

Zab 85