4. Ku kuɓutar da talakawa da matalauta,Ku cece su daga ikon mugaye!
5. “Waɗanne irin jahilai ne ku, wawaye!Kuna zaune cikin duhu,Ga shi, ba adalci a duniya sam!
6. Na faɗa muku, ku alloli ne,Cewa dukanku 'ya'ya ne na Maɗaukaki.
7. Amma za ku mutu kamar kowane mutum,Ku fāɗi kamar kowane basarauce.”
8. Ya Allah, ka zo, ka mallaki duniya,Dukan al'ummai naka ne.