Zab 81:14-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Da sai in kori abokan gābansu nan da nan,In yi nasara da dukan maƙiyansu.

15. Maƙiyana, za su sunkuya a gabana saboda tsoro,Hukuncinsu na har abada ne.

16. Zan ciyar da ku da kyakkyawar alkama,In ƙosar da ku da zuma.”

Zab 81