1. Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah Mai Cetonmu,Ku raira yabbai ga Allah na Yakubu!
2. A fara waƙa, ku buga bandiri,Ku yi waƙoƙi masu daɗi da molaye, da garayu.
3. Ku busa ƙaho domin idin,A amaryar wata,Da a tsakiyar farin wata.
4. Wannan doka ce a Isra'ila,Umarni ne kuma daga Allah na Yakubu.